A yayin tsarin fasalin ayyukan hukumomin sun bayyanawa jama'a ta bakin Malam Lawal Magaji wanda ya kasance ministan ayyukan jin kai na jamhuriyar Nijar.
Yace yin ayyukan na bukatar kudi kimanin dalar Amurka miliyan 271. Kasashen duniya da suka hada da Amurka su ne zasu hada taimakon wajen kashi 65 kana ita ma gwamnatin Nijar ta cike sauran.
Yawancin kudin za'a yi anfani dasu ne a yankin Diffa, yankin da ya sha fama da rikicin Boko Haram.
Dahiru Malam Ligali shugaban majalisar jihar ta Diffa yace galibin mutanen dake noma a jihar rikicin ya rutsa dasu saboda wajen shekaru uku ke nan basu samu sun yi noma ba domin sun bar gidajensu. Idan an taimaka masu zasu gyara muhallansu, su shiga gonakansu su kama aiki.
A jihar akwai makiyaya dake bukatan tallafi kana ga dimbin matasa da ya kamata a kula dasu, a basu horon da zai sa su kama sana'a domin hanasu shiga aikin asha.
Kawo yanzu dai dala miliyan 147 suka shiga hannu inji jagoran hadin gwuiwar ofishin Majalisar Dinki Duniya a Nijar wanda zai kula da ayyukan har sai an gamasu.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.