An magance annobar cuta mafi muni ta biyu a tarihi, a cewar gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ranar Alhamis 25 ga watan Yuni.
Ministan lafiyar kasar ne ya ayyana magance annobar wadda ta barke a watan Agusta na shekarar 2018 a gabashin Congo, ta kuma kashe akalla mutum 2,280, duk da cewa an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar a wani bangare daban na kasar.
Wannan sanarwar na zuwa ne yayin da babbar kasar da ke tsakiyar nahiyar Afirka ke ci gaba da fama da cutar kyanda mafi yawa a duniya, da barazanar karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus da kuma barkewar cutar Ebola a arewacin kasar a kwanan nan.
Annobar cutar ta Ebola ta barke ne a yammaicn Afrika a shekarar 2013 ta kuma lakume rayukan mutane sama da 11,300 a cikin shekaru 3 a kasashen Guinea, Laberiya da Saliyo.
Facebook Forum