Bankin na ganin akwai bukatar kirkiro wata hanyar samun kudin shiga banda man fetur domin kasar ta samu abubuwan cigaba.
Wannan ra'ayin na Bankin Duniya ya zo daidai da na sarkin Kano Muhammad Sanusi II wanda shi ma kwanakin baya yayin da yake jawabi a birnin Legas ya nemi gwamnati ta cire tallafin da take ba man fetur.
To amma it a gwamnati sau tari tana fada bata da aniyar cire tallafin.
Akan shawarar bankin wasu sun furta ra'ayinsu. Wani yace bankin duniya da makamantansa su ne makiyan kasashen Afirka. Kullum abun da zai kara jawowa mutane wahala da fitina a cikin kasa suke kawowa. Cire tallafi fitina ce zai jawo. Wannan yace da zara an cire tallafin wata matsala ce zai haifar ya jefa kasar cikin tarzoma. Saboda haka yace shi bai goyi bayan cire tallafin ba.
To saidai wani yace a gaskiya wasu mutane ne tsiraru suke anfana da tallafin. A duba tallafinn shin talakawa suna anfana dashi inda ko babu to ta yaya za'a gyara lamarin yadda zai taimaki talakawan. Idan kuma talakawa basa anfana to tallafin bashi da anfani.
A wani hannun kuma matsalar karancin man fetur sai kara ta'azara yake yi lamarin da ya kai har masu ababen hawa na shafe awanni a layin mai.
Sau tari akan zargi dillalan man fetur da kawo karancin man. Amma sun musaanta zargin. Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai kula da jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Abubakar A. A. Butu yace matsalar man fetur ta faru ne a kasar baki daya. Kasar tana anfani da lita miliyan arba'in kowace rana amma duk matatun man kasar lita miliyan goma sha tara suke sarafawa kullum. Ke nan babu wadatacen mai a kasar lamarin da ya jawo matsala.
Akan kudin tallafi Alhaji Butu yace masu shigo da man fetur su ne suke karbar tallafi.
Ga karin bayani.