Sakataren kungiyar, Dr. Khalid Aliyu, yace sun tattaro masu goyon baya da wadanda ke yin adawa da aikin rigakafin cutar, suka hallara a Minna Jihar Neja, domin a samar da fahimtar juna, a kawar da irin dari-darin da wasu ke yi.
Cikin wadanda suka halarci wannan taron da kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta kira har da karamin ministan kiwon lafiya da wakilan hukumomin kiwon lafiya na kasa da kasa.
Wakilin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, Mr. Bolaji Buhari, ya bayyana cewa ya zuwa wannan lokaci da ake taron, yara 25 ne aka tabbatar da sun kamu da wannan cuta a jihohi 9 a yankin arewacin Najeriya.
Kwamishinan harkokin ilmi na Jihar Neja, Alhaji Danladi Abdulhamid, ya ce gwamnatin jihar ta lashi takobin cewa in Allah Ya yarda nan da karshen wannan shekara za a daina samun bullar cutar Polio a cikin jihar.
ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.