Shugaban karamar hukumar Okigwe, Mr. Beneth Eliochine ya ce wannan yunkurin babban ci gaba ne ga jihar da kuma sauran ‘yan kasuwa da suka fito daga sauran sassan kasar.
Kasuwar za ta taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa, kana za ta kawo ci gaban kasuwanci tsakanin al’ummar yanki Arewa da na kudu, kuma kasuwace da za ta taimaka matuka wajen ganin an tsaftace muhalli.
Shugaban kungiyar dillalan kayan gwari,Mallam Shugaba Mika’ilu Kigani ya bayyana jin dadinsu da wannan kasuwar, domin zai sa masu sana’ar gwari su dawo kasuwar da zarar an kammala aikinta. Sannan suna kira da jama’ar Arewa masu hannu da shuni da su taimaka musu wajen ganin an kammala gina kasuwar cikin karamin lokaci.
Shi ma Shugaban al’ummar Arewa mazauna jihar ta Imo, Alh. Abdullahi Yaya Biu ya bayyana gamsuwarsa da kasuwar, inda ya ce suna sa ran za ta samar da kyakkyawar dangantakar kasuwanci tsakanin Arewa da kudancin kasar da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar Najeriya ba wai jihar kadai ba.
Domin samun karin bayani sai a saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe.
Facebook Forum