Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Najeriyar suka fitar da sanarwa kan ranar sake bude makarantu ga daliban da za su zana jarrabawar karshe ta WAEC.
Hukumar tsara jarrabawar ta bayyana cewa ranar 17 ga watan Agusta ne za a rubuta WAEC, inda aka baiwa yaran akalla mako biyu don su kimtsa.
Iyaye, dalibai da masana harkokin ilimi da malamai ne suka bukaci a dage ranar rubuta jarrabawar, suna masu cewa mako biyu ya yi wa yaran kadan su shirya yadda ya kamata.
Darektar cibiyoyin zamantakewa a ma’aikatar kula da ayyukan addinai kuma tsohuwar malamar makaranta, Bilkisu Muhammad Kai’kai, ta bayyana wa Muryar Amurka cewa a ganinta yin hakan zai zama takura ga dalibai.
"Idan yara suna gida, yawancinsu ba karatu suke yi ba saboda hakan ya kamata a dan bude makaranta na wani dan lokaci domin su tuna abubuwan da aka koya musu tukuna," a cewar Malama Bilkisu.
"Gaskiya wannan lokacin ya kure sosai, ba a ba mu damar yin shiri yadda ya kamata ba." In ji Tijjani Abubakar, daya daga cikin daliban da za su rubuta jarrabawar ta WAEC.
Binciken da VOA ta gudanar ya gano cewa babu alama an fara saka matakan kariya ga daliban da za su koma makaranta domin jarrabawa a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da ke unguwannin Asokoro, Jabi da Karu a Abuja.
Sai dai Darektan yada labaran ma’aikatar ilimi a tarayyar Najeriya, Ben Goong, ya ce ma’aikatar ilimi za ta kula da aikin aiwatar da dukannin sharudodin da gwamnati ta gindaya domin kare lafiyar dalibai a lokacin jarrabawar.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana matakin na bude makarantu ga daliban azuzuwan karshe domin zana jarabawar WAEC lamarin da ‘yan kasar ke cigaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyin su akai.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti.
Facebook Forum