Har yanzu muna nan akan ibadun da ya kamata a lazimta a goman karshe, baya ga sallar tahajud da itikafi. Akan haka ne wannan karon muka samu bakoncin Goni Warsu Rabiu, gidan maza shugaban makarantar Ma’ahad Sheik Muhammad Harun, mun kuma zanta da shi a kan muhimancin itikafi.
Mun kuma fara da tambayarsa wai shin wane irin abubuwa ne basu hallatta ga wanda yake itikafi yayi su ba?
Ya ce sallar itikafi, sallah ce da ake son mutun baya ga kebance kansa a cikin masallaci yana ibada, tare da ambaton sunayen Allah da karatun alkur’ani domin neman kusanci ga Allah mahallacinsa.
A cikin kwanakin 10 karshe ne ake shiga itikafi, tare da yin biyayya sannan ba’a itikafi sai a masallatan Juma’a, ya kara da cewa ba’a son mai itikafi yana yawan surutu, ko shiga da wasu abubuwan da zasu dauke mishi hankali na rayuwar duniya, ma’ana sanin abinda duniya ke ciki ta hanyar amfani da wayoyin zamani.
Kuma baya hallata ga mai itikafi ya fita daga cikin masallaci ko ya hallarci jana’iza, ko gaida mara lafiya da zarar ya kudirci niyyar zai yi itikafi, lallai zai kauracewa dukkanin wadannan abubuwan, ga mai aure kuma bai hallarta ya kula matarsa ba ko wasu zantuka da zasu sa ya shiga wani yanayi ba.
Facebook Forum