A cikin makon nan ne likitoci 15 daga kasar China da suka hada da masana da kuma kwararru masu kula da majinyata suka sauka a Najeriya, da nufin bada gudunmawa don yaki da cutar Coronavirus a kasar.
Sai dai kungiyar likitocin Najeriya NMA ta nuna rashin gamsuwa da wannan tsari, tana mai nuna tamkar hakan zai kawo koma baya ne ga lamuran harkokin kiwon lafiya a Najeriya.
Shugaban kungiyar likitoci na Najeriya, Dr. Francis Faduyile ya ce, a halin da ake ciki yanzu Najeriya na taka rawar gani a yaki da cutar ta Coronavirus, saboda haka idan ma da bukatar taimakon kasar China, za ta iya taimaka wa ta fannin kimiya da fasaha ba tare da zuwan likitocin ta Najeriya ba.
Ita ma kungiyar kwadago ta TUC, ta bakin kakakin kungiyar Nuhu Toro, ta nuna kin amince wa da gayyato likitocin, yana mai cewa “ita kanta kasar China ba ta fita daga annobar ba.”
Ya kara da cewa, Najeriya na da kwararrun likitocin da zasu shawo kan wannan annoba idan suka samu gudunmawar da ta dace daga gwamnati.
A halin da ake ciki dai yanzu, hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC da kuma likitocin Najeriya suna aiki ba dare ba rana wajen kula da masu dauke da cutar da kuma gwajin wadanda ake zargin suna dauke da ita tare da wayar da kan jama'a kan hanyoyin da zasu bi wajen hana yaduwar cutar ta Covid-19.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum