Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Odion Ighalo, ba zai fara atisaye da sauran ‘yan kungiyar tasa ba, saboda damuwar da ake da ita tun bayan dawowarsa daga kasar China, don tabbatar da cewa bai kamu da cutar Coronavirus ba .
Ighalo ya koma United ne a ranar 31 ga Janairu daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China, duk da cewa babu wani hadari mai karfi a tattare da shi, don garin da ya zauna yana da nisan kilomita dari daga lardin Hubei, wanda shi ne gari na farko da aka samu barkewar cutar, amma kungiyar ta zabi daukar matakin ne don yin taka-tsan-tsan.
United ta kuma yanke shawarar kin daukar Ighalo a sansanin horon lokacin hutu na hunturu a Spain, sakamakon damuwar da yake fuskanta na iya fuskantar wahalar sake komawa Ingila.
Likitoci na bada shawara a kebe r mutanan da suka koma Burtaniya daga wasu kasashe, kamar China,na kwanaki 14.
A cewar kocin United Ole Gunnar Solskjaer, Ighalo zai bi tawagar zuwa Landon a ranar Litinin, inda za su kara da kungiyar Chelsea.
Facebook Forum