Yace idan abubuwa suka tafi cikin gaskiya hakika APC zata ci zabe mai zuwa.
Yace daga bangaren PDP wadda ita ce take da gwamnati da hukumar zabe da kudi da 'yansanda da sojoji idan zata bari a yi zaben cikin gaskiya APC zata ci ko ba dan komi ba domin mutane sun gaji da PDP.
Mutane suna neman canji. Canji kuma yana da anfani. Cikin shekara hudu ko takwas yakamata a dinga samun canji ko wanene ma yake gwamnati. Amma a ce shekara goma sha biyar abu daya ake yi bashi da dadi.
Akan matsalolin cikin gida da APC ke fama dasu Alhaji Tofa yace ana kokarin dinke barakar da ta taso. Ana son 'yan takarar su samu su hada kansu. Idan an je fitar da gwani kowanene ma ya samu su goyi bayansa.
Wakilin Muryar Amurka ya tambaya ko zasu iya kai wajen fitar da gwani cikinsu. Sai yace tana yiwuwa a kai wannan matsayin idan ba'a sami masalaha ba tsakanin 'yan takarar.
Yace 'yan takarar su biyar ne har da wani tsohon dan jarida Sam Nda Ishaya wannda yace mutumin kairki ne da kuma Okorocha, gwamnan Imo. Amma yace duk 'yan takarar mutanensa ne. Yace watakila su zama shida domin Tambuwal ma na iya fitowa.
Sai dai yace sun fi son a yi sulhu maimakon a je fitar da gwani duk da ba'a son a matsantawa kowa ya janye.
Alhaji Bashir yace kowane cikin 'yan takarar ya fi shugaba Jonathan iya aiki da kwarewa. Sun fishi hankali sun kuma fishi kishin kasa.
Ga karin bayani.