Rahotanni daga Najeriya na cewa, Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, ta bayyana cewa ta na neman Gimba Kumo surukin ga Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.
Ana zargin tsohon babban daraktan Bankin Mortgage na Tarayyar a Najeriya mai suna Gimba Kumo bisa zargin karkata akalar dala miliyan 65.
A shekarar 2016 Kumo ya auri yar’ shugaban kasa Fatima Muhammadu Buhari.
Sauran mutum biyun da ake nema sun hada da Tarry Rufus da kuma Bola Ogunsola kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.
A watan Afrilu, kwamitin da ke kula da fannin asusun ma'aikatun gwamnati a majalisar dattawa, ya gayyaci Kumo don ya yi bayani kan wasu kudaden kwangila naira biliyan uku a lokacin yana aiki da bankin.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta ICPC Azuka Ogugua ya fitar a jiya Alhamis, ya bukaci duk wanda ke da bayanai game da inda wadannan mutane uku da ake zargi suke, da ya kai rahoto ga hedikwatar Hukumar ko kuma ofishin‘ yan sanda mafi kusa.
Shi dai Gimba Kumo, ya yi aiki ne a matsayin babban Darakta Bankin Mortgage a karkashin Mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ya kuma kammala karatunsa ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Kuma dan’asalin jihar Gombe ne.
Sai dai ya ’zuwa buga wannan labari fadar shugaban kasar ba ta mayar da martani ba kan zarge-zargen da ake yi masa.