Yanzu haka rundunar ‘yan sandan kasar na kan horas da wasu zababbun mutane a kan aikin kula da tsaro wadanda zasu horas da sauran al'ummomin su, sai dai masana tsaro na ganin ya dace a yi hakan tun da dadewa.
Tun lokacin da matsalolin rashin tsaro suka soma yin kamari a Najeriya mahukunta ke cewa suna daukar matakan magance su, sai dai kuma har yanzu ana samun matsalolin.
A wani yunkuri na kara azama ga kokarin na mahukunta, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umurnin horas da jama'ar kasa dubarun samarwa da wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Horaswar dai tana gudana a fadin shiyoyin yankunan kasar inda mataimakin sufetan ‘yan sanda Ahmad Sani Abubakar ke jagorantar wanda ke gudana a yanki na goma na rundunar dake arewa maso yamma, mai hedikwata a Sakkwato.
Da ma masana aikin tsaro sun ce shirin sanya jama'a ga samar da tsaro abu ne da ke da alkibla a ko'ina cikin duniya.
Kwamishinan ‘yan sanda a Sakkwato Muhammad Usaini Gumel ya ce shi ne manufar da ake son cimma aka shirya wannan taron.
A bangaren jami'an tsaron soji ma suna kara matsa kaimi ga samar da tsaro ta hanyoyi daban daban kamar yadda rundunar ta shimfida wani titi mai tsawon kilo mita daya ga jama'ar Ka'oje ta jihar Kebbi don kyautata rayukan jama'a.
A lokacin kaddamar da bude titin babban hafsan sojin kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya ya ziyarci Sarkin Bargun Ka'oje Mustapha Usman Adamu inda ya jadadda bukatar samun goyon bayan sarakuna da ma jama'a ga samar da tsaro.
Yankin dai na Ka’oje yana da saukin matsalar rashin tsaro, sai dai saboda yanayin dajin da ke wurin basarakin ya roki kafa wani sashe na rundunar Soji a yankin.
Masana lamurran tsaro na ganin wannan yunkuri na jami'an tsaro yana da muhimmanci amma ya dace a yi hakan tun da wuri.
Saurari rahoton cikin sauti: