Sakamakon kuncin rayuwa da suke fuskanta ‘yan gudun hijira a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar, sun zabi sana’ar sarar bsihiyoyi suna sarrafa gawayi da su, al’amarin da kuma ke ci gaba da haddasa kwararowar hamada a jihar.
Hakan ya sa hukumomin da ke kula da kare gandun daji a jihar suka fara daukar matakan ladabtarwa ga duk dan gudun hijirar da aka samu yana gudanar da wannan sana’ar
Shekaru dai takwas kenan da ‘yan gudun hijirar na jihar Diffa ke gudanar da wannan sana’ar ta sarar itace suna kuma sarrafa gawayi su, a cewar Almustafa Abba wani dan gudu hijar dake gudanar da wannan sana’ar, inda ya ce rashin aikin yi ne ya sa suka zabi wannan sana’a domin samun abin da za su kai bakinsu..
Sai dai hukumomin dake kula da kare gandun daji a jihar ta Diffa sun bayyana cewa, ya zama wajibi a garesu su fara daukar matakan ladabtarwa ga duk wanda aka samu yana gudanar da wannan sana’ar,musamman ma idan aka yi la’akari da yadda hamada ke ci gaba da gurgusowa a jihar ta Diffa.
Bincike dai ya nuna cewa, buhu guda mai nauyin kilogram dari na lakume itacen da nauyinsu zai iya kai kilogram 700, kuma hakan babbar barazana ce ga muhalli musamman ma idan aka yi la’akari da shekarun da ‘yan gudun hijirar suka kwashe suna gudanar da wannan aikin.