A Jamhuriyar Nijar da alama harkokin siyasa sun fara tabarbarewa soboda cafke wasu ‘yan adawa da suka shiga yin zanga-zangar da hukumomi suka ce haramtattiya ce.
Shugaban hadakar kungiyoyin da suka shiga zanga zangar, Gamace Mahammadou ya tabbatar da cafke wasu ‘yanuwansu tare da cewa shi kansa yaji hukumomi na nemansa.
Dangane da wadanda aka cafke irin su Diori Ibrahim da Maykol Zodi Gamace Mahammadouya ce basu tantance inda suke ba amma kuma su ba zasu yadda da mulkin kama karya ba a kasarsu.
Injishi ba zasu yadda a kawo masu sojojin wasu kasashen waje a jibegesu cikin kasarsu ba.
Duk da cewa hukumomin Yamai sun sanar dasu cewa zanga-zangarsu haramtaciya ce, mai magana da yawun kungiyoyin ya ce hanasun tamkar mulkin danniya ne da su bazasu amince dashi ba. A cewarsa zasu yi gwagwarmaya sosai domin su kwato ‘yancin kasarsu.
Akan ko shi kansa zai gudu ko ya boye saboda ana nemansa, sai ya ce shi ba zai gudu ba. Yanzu ma suka fara fafutika ta gasken gaske saboda wai kasar tasu ce.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Facebook Forum