Hukumomin lafiya a jihar Kano sun musanta rahotannin dake cewa, sun killace mutane 60 a Cibiyar Kula Da Cututtuka Ta Musamman a jihar bisa zargin sun kamu da cutar Gyandar Birrai biyo bayan samun wani mutum da alamomin cutar a Kauyen Nasarawan Kuki na karamar hukumar Bebeji a jihar ta Kano.
Dr Kabiru Ibrahim Getso kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kano yace ya zuwa yanzu ma’aikatar lafiya ta Kano ta aika samfurin jinin mutunin da aka samu da alamomin kamuwa da cutar ta Gyandar Birrrai zuwa Babban Asibitin Kasa dake Abuja kana daga bisani za’a dauki jinin zuwa cibiyar gwaje gwaje dake birnin Dakar na kasar Senegal domin tantancewa.
Dr Ibrahim Nashabaru, kwararre kan lamuran kwayoyin cutuka dake Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ya bayyana wasu daga cikin siffofin wannan cuta ta Gyandar birrai da kuma matakan da Jama’a ya kamata su dauka domin kare kansu daga kamuwa da cutar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum