Hukumomi a Sudan sun ce ana ci gaba da samun tururuwar jama’a yayinda aka shiga kwana na uku a kada kuri’ar raba gardama kan ‘yancin kudancin kasar duk da kazamin harin da aka kai kan iyakar kudu da arewacin kasar jiya Litinin. Jami’ai sun hakikanta cewa, a kalla kashi sittin bisa dari na masu kada kuri’a a kudancin kasar mai arzikin man fetir zasu kada kuri’unsu, kuri’un da ake bukata domin tabbatar da ingancin sakamakon zaben. Runfunan zabe zasu ci gaba da kasancewa a bude har zuwa ranar Asabar, duk da tashe tashen hankali da ake samu. Wani jami’i a kudancin Sudan yace wasu ‘yan kabilu larabawa sun yiwa wata motar safa dake dauke da masu kada kuri’a kwantan bauna a jihar Khordofan jiya Litinin, suka kashe mutane goma suka kuma raunata wasu takwas.
Hukumomi a Sudan sun ce ana ci gaba da samun tururuwar jama’a yayinda aka shiga kwana na uku a kada kuri’ar raba gardama kan ‘yancin kudancin kasar
![Wata tsohuwa a Kudancin Sudan tana kada kuri'a jiya Litinin a wata mazaba dake birnin Um Durman, Sudan, Jan. 10, 2011](https://gdb.voanews.com/4724464f-73e5-4c03-a408-285964a81168_w250_r1_s.jpg)
Hukumomi a Sudan sun ce ana ci gaba da samun tururuwar jama’a yayinda aka shiga kwana na uku a kada kuri’ar raba gardama kan ‘yancin kudancin kasar.