Hukumar Tashar Jiragen Ruwa ta Najeriya ta gyara ko sake gina wasu makarantu uku da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu.
Hukumar tace ta zabi gudanar da aikin ne domin ba da tata gudummawa ga al'ummar jihar Borno da kuma taimakawa harkokin ilimi a tarayyar Najeriya.
Alhaji Balarabe Umar Samaila babban daraktan hukumar wanda kuma ya wakilci shugaban hukumar Alhaji Hassan Bello shi ya mika makullan makarantun ga kwamishanan ilimin jihar Borno.
Yana mai cewa jihar Borno ta shiga wani hali da kowa ya sani sanadiyar ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram da suka kone ko lalata makarantun jihar. Injishi, hukumarsu ta kan duba hanyoyin da za ta taimakawa al'umma dalili ke nan suka shiga Borno su taimaka ganin cewa wasu ma daga kasashen waje suna kawo taimako.
Gwamnatin jihar Borno ta bakin kwamishanan ilimi Musa Inuwa Ko na cewa tallafin tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama saboda ya zo masu a daidai lokacin da suke bukata musamman idan aka yi la'akari da yawan makarantun da 'yan ta'adda suka lalata.
Makarantun da aka gyara a cikin Maiduguri zasu taimaka yara su koma karatu. Bugu da kari hukumar tashar jiragen ruwan Najeriya ta yi alkawarin gyara wasu makarantun dake jikin jihar.
Kwamishanan ilimin jihar yayi anfani da zarafin da ya samu ya kira wasu hukumomi da kungiyoyi da wadanda Allah ya huwace masu su tashi su taimaka saboda bai kamata a bar wa gwamnati ita kadai harkokin ilimi ba.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum