Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Tayi Wawan Kamu A Filin Jiragen Sama Na Kasa da Kasa dake Abuja


 Kwandan NDLEA na filin jiragen sama dake Abuja, Alhaji Hamisu Lawan
Kwandan NDLEA na filin jiragen sama dake Abuja, Alhaji Hamisu Lawan

Yayinda yake yiwa Muryar Amurka bayani akan kamun da hukumar NDLEA tayi Kwamandan Alhaji Hamisu Lawan yace duk lokacin da jirgin sama ya taso daga Brazil ana jaddada masu su sa ido akan fasinjan da ya taso daga kasar saboda tayi kamarin suna a kan fatauci da miyagun kwayoyi

Inji Alhaji Hamisu Lawan hodar iblis da ake sarafawa a kasar Colombia ta Brazil take shigowa kafin ta isa wasu kasashe.

Yace yawancin kame-kamen da suke yi hanyar da suka fi biyowa ke nan. Yace kodayaushe ana gaya masu su ankara da duk wanda ya shigo jirgi daga Brazil saboda haka ashirye suke su binciki irin wannan dan talikin.

Abu na biyu da ya zaburar da hukumar mutumin takalma ne ya shigo dasu wadanda farashinsu a Najeriya bai taka kara ya karya ba. Idan an yi la'akari da kudin da ya kashe daga Najeriya zuwa Brazil babu yadda zai fitar da kudinsa idan sayar da takalman zai yi.

Abun mamaki duk takalman da aka sasu cikin naura suna dauke da hodar iblis da aka boyeta ta yadda idanu ba zasu ganota ba.

An kiyasta hodar iblis din da aka samu tare da mutumin zata kai dalar Amurka miliyan hudu da dubu dari bakwai.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG