Bisa ga cewar Hukumar, cin abincin da ya kamata da rage cin gishiri da kuma rage shan giya na taimakawa wajen hana kamuwa da hawan jini. Haka kuma rage kiba da shan taba.
Hukumar lafiyar ta bayyana haka ne a daidai lokacin da ake shirin yin bukin ranar lafiya ta duniya. Hukumar lafiyar ta bayyana cewa, hawan jini yana kawo bugun zuciya ko shanyewar jiki ko cutar koda. Yana kuma kai ga makanta, idan ba a yi maganinshi ba. Wannan kuma yana iya kaiwa ga mutuwa. Ciwon suga yana kara sa hawan jini ya zama da matsala.
Bincike ya nuna cewa, an sami raguwar hawan jini da bugun zuciya a kasar Japan ta dalilin zuwa asibiti a kai akai domin gwajin lafiya da kuma kamfen wayar da kan jama’a game da kiwon lafiya.