Kanal Hamidu Ali shugaban hukumar kwastan ta Najeriya yace daga yanzu hukmar ba zata lamuncewa duk wani jami'inta da aka kama da laifin cin hanci da rashawa ba.
A wani bangaren kuma shugaban ya ja kunnuwan 'yan kasuwa masu shigo da kaya daga kasashen waje da su bi hanyoyin da suka dace musamman wurin biyan kudaden harajin shigo da kaya kasar.
Shugaban yace yawan shigo da kaya ta barauniyar hanya shi ya jawo wasu matsalolin da ake fama dasu yanzu a Najeriya musamman ta fuskar harkokin tsaro..Saboda haka yace duk wani jami'in kwastan da aka samu da cin hanci da kuma yin chuwa-chwa to ya kuka da kansa.
Yace shugaban kasa ba boyayye ba ne a wurinsu.Sun san akidarshi sun kuma san manufarshi. Daga yanzu hukumar zata hukunta duk wanda yake da hannu a cin hanci da rashawa. Yace mai bada cin hanci da mai karbar duk laifinsu daya. Dukansu za'a hukunta.
'Yan kasuwan arewa maso gabas sun bayyana abubuwan da suke bukata daga hukumar ta kwastan. Alhaji Dauda Saidu Memba shi yayi jawabi a madadin kungiyar 'yan kasuwa da suka gana da shugaban hukumsr kwantan din.
Ya roka a taimaka masu saboda matsalar da suka samu sanadiyar rikicin kungiyar Boko Haram.
Ga karin bayani.