Dubun-dubatar mutane a Najeriya dama kasashen duniya, na ganin cewa abun da hukumar zabe ta kasar Najeriya wato INEC tayi, dangane da dage babban zabe da aka shirya za’a gudanar a wannan watan, da ta kara makonni shida, ba abu ne mai alfanu ga siyasar Nageriya ba. Ganin cewar duk ilahirin hujjojin da shi shugaban hukumar Attahiru Jega ya bada, ba wasu hujjoji kwarara bane.
Ta bakin wani masani a harkar siyasa Dr. Abbati Bako, na cibiyar harkokin demokaradiyya na kasa-da-kasa, yana ganin wannan cin zarafin siyasa ne kawai. Dr. Bako na gani idan har hukumar zata ce wai saboda rashin tsaro a kasar ne yasa ta dage wannan zaben, to gaskiya wannan bai yi dai-dai ba, a nashi ganin ai akwai kasashe, kamar su Siriya, Ukiren Libiya da dai ire-irensu, da dama da suka samu kansu cikin wasu irin munanan halaye na rashin tsaro wanda ma wasunsu suna cikin yaki, amma duk da hakan bai hana su gudanar da zabe ba da cigaba da mulkin demokaradiyya.
Dr. Abbati, dai yana ganin ai ya kamata ace ita hukumar zabe da duk masu ruwa da tsaki su san wannan matsayin tun da dadewa, amma ba sai da zabe yazo sauran kwanaki kadan ba, don haka ya kamata ace sun fahimtar da mutane tun da wuri kuma sunyi kyakyawan shiri mai tsari.
Mr. Bako ya kara da cewa ai Najeriya nada mazabu dubu dari da ishirin, kana tana da yawan kananan hukumomi dari bakwai da saba’in da hudu, da jihohi talatun da shida da Birnin Tarayya, to alal hakika koda kananan hukumomi ashirin ne ke fuskantar wadannan matsaloli, to bai kamata a dage zaben ba, wanda zai shafi sauran, gaskia wannan yasabawa ka’idoji na demokaradiyya.
A karshe Dr. Abbati Bako na ganin idan har dai wadannan kasashen zasu iya gudanar da zabe a cikin irin halin yaki to lallai babu dalilin da zai sa ba za’a iya gudanar da zabe a Najeriya ba. Yana ganin cewar bai kamata a tauye wa masu rinjaye hakinsu ba, don biyan bukatun marasa rinjaye.