Hukumar zaben Najeriya mai zaman kan ta, INEC a takaice, ta bada sanarwar dage aikin raba katin rajistar zaben da ta shirya farawa Jumma'ar nan a jahohin Naija da Katsina da Kaduna da kuma Borno.
Yanzu dai hukumar zaben ta INEC ta ce sai ranar 28 ga watan nan na Nuwamba za ta fara wannan aiki.
Domin jin dalilai ko matsalolin da suka sa Hukumar zaben daukan wannan mataki na canza lokacin fara raba katin rajistar zaben a jahohin Naija da Katsina da Kaduna da kuma Borno wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya tuntubi kakakin hukumar zaben Mr.Nick Dazang wanda yayi karin haske kamar haka:
Duk da bayanin da hukumar INEC ta yi, 'yan jam'iyyar APC ta adawa a kasar Najeriya na ganin cewa akwai wata boyayyar manufa kuma akwai wani shirin neman kuntata mu su.