Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin kan INEC ta maida wasu jam’iyyu 22 matsayinsu na kasancewa jam’iyyun siyasa da za su iya tsayawa takara, amma INEC ta ce ta na kan bakarta ta dakon hukuncin kotun kolin kasar.
A cikin watan Fabrairun shekarar 2020 ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta bayyana matsayinta na soke jam’iyyu 74 sakamakon rashin samun nasara a zaben shekarar 2019 da dai sauran wasu dalilai masu nasaba da rashin cika wasu shrudoddin yin rajista a matsayin jam’iyyu, inda jam’iyyun suka garzaya kotu daga bisani.
Hukumar INEC, ta bakin kakakinta, Mal. Nick Dazan, ta sake jaddada cewa, ta na kan bakarta ta dakon hukuncin kotun koli kafun ta dauki matakin gaba baya ga hukuncin kotun daukaka kara na maida wasu jam’iyyu 22 kan matsayinsu na jam’iyyu.
Fitaccen Lauya, Barista Mainasara Kogo ya bayyana ra'ayinsa kan hurumin doka game da wannan matsayin na INEC.
Umaru Muhammad Mai Zabura, shugaban Jam’iyyar NDLP da ke daya daga cikin jam’iyyun da Hukumar INEC ta soke, ya ce bai kamata INEC ta ki mutunta umarnin kotu na sake maida wasu jam’iyyu kan matsayinsu na iya tsayawa takara kamar yadda ya ke a da ba.
A nasa bangare, tsohon dan takarar Shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyya Labour party, Mal. Usman Zaki Muhammad, bai kamata a samu jam'iyyu barkatai a kasar ba, ya na mai goyon bayan soke wasu jam'iyyun saboda rashin tasirinsu.
INEC dai ta kara jaddada cewa, jam’iyyu 18 ta ke sane da su wadanda za su iya tsayar da ‘yan takara kamar yadda dokar zabe ta tanadar.
Duk kokarin jin ta bakin sauran jam’iyyun da INEC ta soke kan lamarin dai ya ci tura.
Saurare cikakken Rahoton a Sauti: