Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta kara inganta yawan wasu kyaututtuka guda biyu da za ta rika baiwa a bangaren wasan kwallon kafar da take shiryawa na ajin Mata.
Hukumar ta FIFA tace wannan matakin shi zai tabbatar da daidaito tsakanin bangaren Maza da Mata a fagen kwallon kafa na kyaututtukan da take bayarwa duk shekara.
Karin sabbin kyaututtukan da hukumar ta kara sun hada da karrama Mace mai tsaron raga da ta yi fice, wato Best Goalkeeper a turance sai kuma (Best Team) tawagar Mata, mafi kwazo yayin bikin kyaututtukan da take badawa a duk shekara.
A wannan shekarar za'ayi bikin bayar da kyaututtukan na hukumar FIFA ne a birnin Milan, dake kasar Italiya ranar 23 ga watan Satumba 2019.
Inda a ranar 7 ga watan Yunin bana za a fara gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ajin Mata, wadda kasar Faransa zata karbi bakoncin sa.
Facebook Forum