Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Ingila taci tarar tsohon dan wasan Manchester United, Paul Scholes kudi fam dubu 8,000 bayan da ya
amince cewar ya karya ka'idojin yin cacar kwallon kafa.
An tuhumi tsohon dan wasan kasar Ingila Scholes ne da yin caca kan wasu wasannin tamola 140 da akayi tsakanin 17 ga watan Agustan 2015 zuwa 12 ga watan Janairun shekara 2019.
Bayan haka kuma hukumar kwallon kafar Ingila ta gargadi tsohon dan wasan da ya kaucewa duk wata hanyar da zata sake sashi aikata laifin nan gaba.
Scholes ya bayyana cewar yana neman afuwa kan laifin da yayi, ya kuma amince da tarar da hukumar FA ta kasar Ingila ta yi masa.
Tsohon dan wasan ya cigaba da cewa wannan babban kuskure ne da ya aikata a rayuwarsa, kuma bada gangan yayi ba, baya fatan haka ya sake faruwa.
Facebook Forum