Abdoulaye Madassane Alkika na daya daga cikin masu kidar garaya dake tare da wasu matan abzinawa mawaka su uku da suka fara kawo ziyara a nan Amurka daga Jamhuriyar Nijer.Mata mawakan sun zagaye jihohin Amurka inda suka rera wakokin gargajiya domin nishadatar da masu kallo.
Fatou Seidi Ghali itace ba-Abzina ‘yar asalin Illighadad ta farko da ta kafa irin wannan tawagar mawaka mata mai suna "Les Filles de Illighadad". Mawakan ‘yan asalin Illighadad wani karamin garin dake Saharar jihar Abalak ta jamhuriyar Nijar, sun zagaye kasasen duniya daban-daban domin tallata wakoki da al’adu, haka zalika suka rera wakokin a sashen ajiyar litattafai na majalisar tarayyar Amurka.

Facebook Forum