Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hotunan Ziyarar Shugaban Najeriya Muhammad Buhari zuwa Amurka Watan Yuli 19-20, 2015

Kadan daga cikin hotunan shugaban Najeriya Muhammad Buhari akan ziyarsa zuwa nan Amurka inda ya gana da shugaban Amurka Barack Obama da wasu kusoshin gwamnatin Amurka da shugabannin masana'antu.

Kadan daga cikin hotunan da Muryar Amurka ta dauka akan ziyarar shugaban Najeriya zuwa nan Amurka. Mai masaukin shugaban Barack Obama ya saukar dashi ne a gidan nan mai dimbin tarihi da ake kira Blair House wanda yake duban Fadar White House.
Shugaba Buhari ya shiga tarihi domin ba kasafai Amurka ke saukar da shugaban wata kasa a Blair House ba.
Kodayake tarihi ya nuna firayim ministan Najeriya na farko Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa an taba saukar dashi gidan, amma kawo yanzu babu wani shugaban kasar Najeriya da ya sauka Blair House. Najeriya ta shiga tarihi kuma shugaba Buhari ya kawo mata tagomashi, ta zama kasar da duk manyan kasashen duniya ke son yin harka da ita saboda sabon shugabanta da suke ganin cewa yana da adalci kuma zai yaki cin hanci da rashawa abubuwa biyu da suka yiwa Najeriya katutu.
Shugaba Buhari ya jaddada aniyarsa na yakai Boko Haram da duk wani aikin ta'adanci a kasar ko ta halin yaya.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG