A kalla mazauna kauyen Kawuri dake arewa maso gabashin Najeriya, su 85 ne suka gagara guduwa daga mahara wadanda suka fasa bom a wata kasuwa dake ci mako-mako, kuma suka kona gidaje a kalla 300, inji wani jami’I yau Talata. Maharan sun bar nakiyoyi a kasuwar, wadanda suka fashe washegari.
Hotunan Wurin da Ake Zaton ‘Yan Boko Haram Sun Kai Wa Hari, Junairu 28, 2014, Babi na 2

1
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a lokacin da yake ziyartar mutanen da suka ji raunuka a wani asibiti, bayan harin da 'yan bindiga suka kai Kawuri Junairu, 28 2014.

2
Wasu gidaje da aka kona a harin da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kaishi a Kawuri dake Maiduguri, Junairu 28, 2014.

3
Ana yi wa wani mutum magani a rauninsa a asibitin Konduga bayan harin da aka kai daga wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Boko Haram ne a Kawuri dake Maiduguri, Junairu 28, 2014.

4
A woman with her children pack what is left of their belongings, following an attack in Kawuri January 28, 2014.