Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hotunan Kan Kwalin Sigari Na Iya Sa Mutane Daina Shan Taba


Kwalayen sigari
Kwalayen sigari
Wani bincike da aka gudanar a kasar Canada ya nuna cewa, yana yiwuwa irin hotunan gargadi da aka buga a kwalin taba sigari ya sa wadansu mutane daina shan taba saboda tsoron kamuwa da cutar kansar mara.

Binciken da aka gudanar kan mutane 291 ya nuna a ofishin wani likita dake birnin Toronto na kasar Canada ya nuna cewa, galibinsu basu san shan taba yana iya sa mutum ya kamu da cutar kansar mara ba sai lokacin da suka ga hotonunan da aka buga a kwalayen taba domin wayar da kan jama’a.Masu binciken sun ce shan taba sigari ne sanadin tsakanin kashi talatin zuwa hamsin na cutar sankaran mara.

Kasar Canada ta kafa dokar da ta tilasa kamfanonin taba sigari su rufe kashi saba’in bisa dari na kwalaye taba da hotunan wadanda suka kamu da cututuka ta dalilin shan taba domin gargadin masu sha. Wani yunkurin da bai cimma nasara ba a Amurka.
Cutar kansar mara tana daya daga cikin kansa da maza suka fi kamuwa da ita a Amurka. Cibiyar nazarin cutar kansa ta Amurka tayi kiyasin cewa, kimanin Amurkawa dubu saba’in da biyu da dari bakwai da hamsin ne za a samu da cutar kansar mara a shekarar nan ta dubu biyu da goma sha uku, mutane dubu goma sha biyar da dari biyu da goma kuma zasu mutu ta dalilin cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG