Kamfanin Microsoft ya ba masu nazari da saka jari mamaki ranar 24 ga watan Oktoba yayin da ya bayyana samun Karin kaso 17 cikin 100 kan ribar da ya ci cikin watanni uku da suka gabata. Karin ribar ya zo ne lokacin da kamfanin ya yi wasu sauye-sauye inda ya rabu biyu da wani rabin na kula da fasahar sarafa abubuwa da daya rabin kuma na kula da kayan da masu ciniki ke saya yau da kullum.