Shugaban hukumar ta Hisbah, Muhammad Ibn Sina, ya ce amfani da mutum mutumin ya sabawa dokar Musulunci.
Ya kuma kara da cewa tuni ma’aikatan hukumar za su fara safarar duk wanda aka kama da ya saba dokar za su hukunta shi.
Muryar Amurka ta zanta da wasu masu shaguna sayar da kayayyaki kan yadda suka karbi wannan sabon doka.
Muhammadu Subha ya ce wannan sam bai dace ba saboda kasar mulkin dimokradiya ne ba mulkin Musulunci ba ne.
Shi kuwa Abubakar Aliyu Ababakar ya ce wannan zance bai yi dadi ba domin ita kanta sana’a ai jihadi ne, mutum yana sana’arsa ne domin ya rufawa kansa asiri sannan ana kokarin cewar ba zai yi da amfani da wani abu ba wajen tallata hajjarsa ba.
Abba Dan Arfa shi ma ya ce akwai matsalolin da dama da ya kamata a dakile, ba a zauna ana zancen hana amfani da babin roba ba wanda da shi ne suke samun kwastamomi da za su ga kayansu har su yi sha’awar saya’
To ko ya hakan zan shafi tattalin arziki masu irin wannan sana’a?
Farfesa Mustapha Muktar na sashin tattalin arziki Jami'ar Bayero ta Kano ya ce hakan zai kawo canjin yanayin tallata kayayyakin da masu shaguna da teloli ke yi kan hanyoyi da shaguna, sannan zai kawo musu koma baya wajen cinikayyarsu saboda ba za su iya tallata su a waje a gani ba.
Ya ce idan masu shaguna za su yi amfani da mutum-mutumin ba tare da yana dauke da kai ba, to babu laifi, amman idan mutum mutumin yana da kai a tare da shi - ma’ana yana da suffar mutum, to lalle ya sabawa doka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: