Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya yi hira ta farko da Muryar Amurka kan batutuwan da su ka shafi wannan nadin da aka masa da kiuma wasu muhimman batutuwa masu alaka.
A hirarsa ta farko a matsayinsa na Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu ya fara da gode ma Allah sannan ya jaddada farin cikinsa, ya na mai danganta wannan nadin da kaddarar Allah.
Ganin rabon wannan gida na Mallawa da sarautar Zazzau ya kai wajen shekara 100; da aka tambaye shi yadda ya ke ganin sake dawowar sarautar Zazzau gidansu, sai Mai Martaba ya kara yin hamdala ga Allah madaukaki. Ya kara bayanin cewa idan aka shiga watan gobe (Nuwamba) zai kasance shekaru 100 rabon gidan da sarautar Zazzau. To sai dai, kamar yadda aka sani, nadin ya faru kafin cikar hakan.
Ya ce kakansu, Malam Aliyu Dan Sidi ne Sarkin Zazzau na karshe daga gidansu, shekaru wajen shekaru 100 da su ka gabata, kafin Allah ya kaddara sarautar za ta dawo masu kuma ya zama sarki.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli ya bayyana cewa kakansu Malam Musa Bamalli ne ya karbo tutar Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio.
Sai dai Mai Martaba Sarkin Zazzau na 19 din ya ce da can burinsa shi ne mahaifinsa ya zama Sarkin Zazzau a maimakon shi amma sai Allah ya kaddari akasin hakan, ya na mai kara yin hamdala ga Allah.
Da aka tambaye shi kan abubuwan da su ka gabaci nasarar da yayi na samun sarautar, sai ya ce haka sha’anin sarauta ya ke; y ana mai jaddada cewa gidajen Sarautar Zazzau na da alaka da juna, don haka, ya ce nasararsa narace ce ta dukkansu. Hasali ma, inji shi, ya na auren diyar marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris.
Mai Martaba Sarki Ahmad Bamalli ya yi kiran da a cigaba da zumunci tsakanin gidajen sarautar ta Zazzau. Ya kara da cewa, “Ba wai don a fafata wajen nemar sarauta, an yanke hulda kenan ba. Wajibi ne a garemu mu duba su, mu rike su bisa amana - saboda mutum – ka dauki Alkur’ani Mai Tsarki ka rantse – kai, ko ma ba ka dauki Alkur’ani ka rantse ba -- idan an rantsar da kai cewa za ka yi adalci, sannan kuma za ka rike mutane bil hakki to wannan ya zama farali a kanka ka rungumi kowa da kowa.”
Ga wakilinmu Isah Lawan Ikara da hirar:
Facebook Forum