Yana da wuya matuka ace an sami dukkan ‘yan takaran shugaban kasa biyu su kasance a cikin birni guda kuma a lokaci guda – kuma a ranar zaben shugaban kasa! Amma kuma sai gashi birnin New York ya hada irin wannan haduwar kuma a daidai lokacinda ake zuwa kakar kyamfe da ta kawo rabuwar kawunan Amurka da aka dade ba’a ga irinta ba a tarihin siyasar kasar Amurka.
Akwai suruttan da ake yadawa cewar mai yiyuwa a sami tsokanar masu kada kuri’a wadanda kuma zasu iya fusata, gashi kuma daman magoya bayan Trump sunce zasu tada kayar baya idan dan takararsu bai yi nasara ba.
Bugu da kari hukumomi na nazarin rahottanin da aka bada dake cewa mai yiyuwa ne kungiyaral-Qaida na barazanar kawo wani hari a lokacin zaben na shugaban kasa.
Barazanan harin na auna jihohi kamar New York da Virgina da kuma Texas, a cewar jami’ai.
Jami’an birnin New York sun ce zasu tattance gaskiya wannan barazana kuma su duki matakan da suka kamata don tinkarar ta..