Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hikimar maida rundunar tsaron Najeriya zuwa Maiduguri


JANAR BURUTAI yana mika takardar aiki ga sabbin kwamandojinsa
JANAR BURUTAI yana mika takardar aiki ga sabbin kwamandojinsa

Boko Haram ita ce babbar matsalar tsaro a halin yanzu a Najeriya har ma da wasu makwabtan kasashen Afirka ta yamma. Bukatar ‘yan wadannan kasashen ita ce magance matsalar.

A yanzu haka rundunar tsaro ta sojojin Najeriya ta tare a Maiduguri bisa umarnin sabuwar gwamnati. Tun rantsar da zabebben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata na shekarar nan ta 2015, Shugaban ya bada umarnin maida rundunar tsaron sojojin Najeriya da ke Abuja kacokan zuwa Maidugurin Jihar Borno.

Kamar yadda Buharin ya fada, ba shi da bukatar da ta wuce a yaki matsalar ta’addanci don samun zaunar da kasa lafiya. Shi menene hikimar da ke cikin wannan ciccibar da akawa Sojojin zuwa jihar gabashin Najeriyar mai fama da matsalar ‘yan Boko Haram da kullum ake asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar?

Sannan da ta yaya Sojojin ke karbar umarnin aiwatar da aikinsu, da kuma yadda yake a yanzu? Kanar Rabe Abubakar da Kanar Sani Usman Kukasheka masu Magana da yawun Sojojin Kasar sun yiwa Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina bayanin hikimar yin haka a rahoto cikin murya da ke kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG