Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya yace mutane 32 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a dimokuradiyyar jamhuriyar Congo.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq yace an sami mutum daya da ya tsallake rijiya da baya daga cikin mutane 33 dake cikin jirgin lokacin da ya fadi, yayinda yake kokarin sauka jiya Litinin a Kinshasa babban birnin kasar Congo.
Hukumomin sun ce jirgin yana kokarin sauka ne yayinda ake tafka ruwa, lokacinda ya dira ba shiri a hanyar saukar jirgin ya yi rugurugu.
Akasarin wadanda suke ciki jirgin fasinjoji ne. Jirgin ya taso ne daga birnin Kisangani dake arewa maso gabashin kasar Congo.