Gwamnatin jihar Kaduna ta sunayen fasinjojin da ke cikin jirgin da aka kai wa hari a ranar Litinin.
Gwamnatin ta karbi sunayen ne daga hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC, hade da cikakken bayanin fasinja na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna mai lamba AK9.
Bayanan sun nuna cewa fasinjoji 398 ne suka sayi tikitin tafiya, amma 362 aka tabbatar da sun shiga jirgin ta hanyar da aka sani.
Wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan kula da tsaron cikin gida na jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan ne ta bayyana hakan.
Wannan adadi bai haɗa da ma'aikatan hukumar ta NRC da jami'an tsaro waɗanda ke cikin jirgin ba.
Yanzu haka an gano gawarwaki takwas, sannan mutum 26 sun jikkata yayin da ake kokarin gano inda sauran fasinjojin suke.
Har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano matsayin fasinjojin da ke cikin jirgin da har yanzu ba a san ko su waye ba a lokacin da aka samu wannan labarin..
Ana bukatar al’ummar kasa da su tuntubi Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna ta wayar tarho 09088923398, domin yin tambayoyi ko bayar da bayanai dangane da fasinjojin da ke cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna mai lamba AK9.