Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Al’umar Borno Na Da Bukatar Tallafi - Kungiyoyi


Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)
Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)

Wasu kungiyoyin ba da tallafi masu zaman kan su, sun ce har yanzu da sauran rina a kaba a garuruwan da ambaliyar ruwa ta shafa kuma al’umomin garuruwan na bukatar taimakon al’uma a ciki da wajen Najeriya.

A daidai lokacin da wasu ‘yan gwagwarmayar nemawa al’umma adalci daga hannun gwamnati ke yin kira ga masu ba da tallafi da su daina kai wa gwamnatin jihar Borno kai tsaye, a bisa zargin cewa an fara karkatar da kudadden da aka samu ya zuwa yanzu.

Wasu kungiyoyin ba da tallafi masu zaman kan su sun ce har yanzu da sauran rina a kaba a garuruwan da ambaliyar ta shafa kuma al’ummomin garuruwan na bukatar taimakon al’umma a ciki da wajen Najeriya.

Da tsakar daren ranar Litinin 9 zuwa asubahin Talata 10 ga watan Satumbar nan ne, al’ummar birnin Maiduguri, Jere da wasu sassan jihar Borno, suka tsinci kan su cikin ambaliyar ruwa da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi, lamarin da ya zuwa yanzu mutanen garuruwan na cikin wani yanayin firgici da ban tausayi kuma ake ci gaba da nema mu su tallafi a ciki da wajen Najeriya.

Wani yanki da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya (Hoto: X/NEMA)
Wani yanki da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya (Hoto: X/NEMA)

Ko wani yanayi al’umar birnin Maiduguri da wasu sassan jihar Borno ke ciki a yanzu, jagorar kungiyar BOWDI mai rajin tallafawa ci gaban mata kuma tsohuwar jagorar asusun tallafi na Malala a Najeriya, Hajiya Fatima Yerima Askira, ta ce akwai sauran rina a kaba kuma wurare da dama mutane na da bukatun da ya kamata a biya musu.

Shi ma shugaban gidauniyar ba da tallafin gaggawa wato Swift Relief Foundation, Abdulaziz Mala, ya yi kira ga kungiyoyin fararen hula da su bibiyi batun tallafin da aka samu kuma ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi abun da ya dace.

Da muka nemi jin ta bakin gwamnati halin da ake ciki na ci gaba da kai wa al’umma dauki musamman bayan irin tallafin kudi da aka samu daga ciki da wajen Najeriya, kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, Farfesa Usman Tar, ya ce gwamnati ta bude asusun ba da agaji kuma ta na yin iya bakin kokarinta don kawo wa al’ummar da iftila’in ya rutsa da su sauki.

BORNO: Hukumar NEMA ta bai wa gwamnatin jihar Borno kayan abinci don rabawa
BORNO: Hukumar NEMA ta bai wa gwamnatin jihar Borno kayan abinci don rabawa

A wani bangare kuma jagoran kungiyar bibiyar al’amurran gwamnati ta Follow the Money, Mukhtar Modibbo, ya ce suna kan shirye-shiryen aika wasikar neman bayani a kan yadda gwamnati ta fara rabon tallafi ga al’umma, don tabbatar da cewa tallafin da aka samu ya kai ga ainihin mabukata a cikin yanayin da ake ciki.

Alkaluman kididdiga dai sun yi nuni da cewa, tun farkon labarin kai tallafi ga gwamnatin jihar Borno ne ya sa wasu kungiyoyi da fitattun mutane a dandalin sada zumunta suka fara yin kira a sa ido kan yadda gwamnati za ta yi amfani da kudaden tallafin da aka samu don gudun kar a karkatar da su.

Saurari cikikakken rahoton Halima Abdulrauf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG