Akwai jan aiki a gaban kamfanonin sadarwar zamani, wajen hada kan al’umar duniya. Mussamman yadda mutane zasu kyautata danganta a tsakani, ta hanyar amfani da kafofin sadarwar zamani don inganta zaman takewar yau da kullun.
Daya daga cikin hanyoyin da suka kamata kamfanonin su dauka shine, wajen kara zurfafa bincike akan rauni da ‘yan adam ke da shi, da kuma fito da hanyar da za’a taimaka musu wajen shawo kan matsalar.
Tristan Harri da Aza Raskin, da suka kirkiri kungiyar dake yaki da cin zarafin bil’adama a kafofin zumunta na yanar gizo, sun bukaci kamfanonin wayoyi da na zumunta su fito da wasu hanyoyi da za’a rage adadin lokaci da mutane ke kashewa akan wayoyin su.
Wannan na daya daga cikin hanyoyi da za’a rage yadda ake cin zarafin mutane ta kafofin, a duk lokacin da mutane suka shiga cikin wani aiki da zai dauke musu hankali za’a samu saukin aikata ayyukan assha a kafofin sadarwar zamani.
Facebook Forum