Da can ko da soja mutum bai isa ya bi hanyar ba domin 'yan Bok Haram zasu hallakashi.
Amma cikin watanni uku an samu canji duk da muguwar barnar da 'yan ta'adan suka tafka a garuruwan yankin. Sojojin Najeriya sun yi aiki matuka sun samu sun kwace wuraren har hanyar ta samu.
A matakin gwamnati zasu sake gina wuraren da 'yan ta'ada suka lalata tare da sake gina wuraren jam'an tsaro domin a tabbatar da tsaro a garuruwan da aka kwato. Da zara tsaro ya samu mutane zasu samu kwarin gwuiwar komawa garuruwansu su cigaba da rayuwarsu.
Gwamnati da al'ummar Borno na harsashen nan da zuwa rabin shekara mai zuwa kowa da kowa zai koma garinsa.
Garin Bama dai ya zama kufai saboda bayan wadanda aka kashe wasu da suka samu suka tsere da rayukansu ko suna zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a Miaduguri ko kuma suna tare da 'yanuwansu. Yanzu a Maiduguri akwai 'yan gudun hijira kimanin miliyan biyu.
Ga karin bayani.