Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankulla Sun Karkata Kan Yan Siyasa Dake Sauya Sheka A Kasar Daga Jam’iyu Daban Daban


APC, PDP
APC, PDP

Batun sauya sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya ga 'yan siyasar Najeriya ba wani sabon abu bane inda kuma da daman yan siyasa, da ake zargi da yin rawa da bazar jama’a, musaman wadanda suke wakilta a matakin daban daban a kasar.

Siyasar shekara ta 2023, dai siyasa ce dake fuskantar sauya shaka. A baya bayan nan, gwamnan jihar Ebonyi Dave Omahi, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kawo yanzu dai ana cigaba da samun manyan 'yan siyasa dake sauya sheka inda bayanai suka nuna cewar, a majalisar Dattawan Najeriya, a kalla sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga jami’iya mai mulki ta APC zuwa PDP mai adawa. Daga ciki kuwa har da Sanata Francis Alimikhena daga jihar Edo, dake kudancin kasar.

Muryar Amurka ta ji ta bakin wani dan jihar Shimee Silvanus, dangane da wannan dambarwa inda yace "Mafi yawacin 'yan daban daban ba ayi masu adalci ba a yayin zaben fitar da gwani da ya gabata ina ganin wannan shine babban dalili da yasa suke ficewa daga jam’iyya zuwa wata jam’iyyar. Haka kuma wasu 'yan siyasa suna sauya sheka saboda ra’ayin su ba don ra’ayin jama’a su ba."

Shima wani dan takarar gwamna kuma jigo a jam’iyyar APC Alh. Abubakar A. A. Gumbi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Alh. Abubakar A. A. Gumbi ya ce "mun yanke shawara ni da jama’a ta a APC mu koma jami’iyar PDP kuma babban dalilin mu shine rashin adalci da kuma rashin iya gudanar da mulki, kuma wanda ke jagorantar APC kamar ba dan siyasa bane abinda dan siyasa ke bai wa kowa hakkinsa."

Mun kuma tuntubi mai sharhi kan harkokin siyasa Prof. Yahaya Tanko baba shugaban sashen nazarin kimiyar siyasa a jamiar Usmanu Dan Fodiyo ko yaya suke kallom sauya sheka da yan siyasa keyi a yanzu.

A cewarsa wannan abu ne wanda ake hasashe musaman ma ganin cewar kamin a gudanar da zabuka na jam’iyyu tare da zaben fidda gwani akwai riginginmu da yawa a mataki na kasa da na gwamnoni da na 'yan majalisu, da kuma abinda ya shafi takarar shugaban kasa.

Saurari cikakken rahoton Abubakar Lamido Sakkwato cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG