Hana safarar bakin haure da hukumomi suka yi a yankin Agadez ya kawo koma baya a wani bangaren tattalin arziki a jihar.
Mafi yawan masu anfani da sarafa kayan da bakin hauren ke saya kafin su cigaba da tafiyarsu suna zaune hannu biyu saboda babu kasuwa.
Abdalla Malufiya dan caga na bakin haure ya bayyana yadda hana bakin ya yi tasiri a wajensu. Yana mai cewa illar da lamarin ya yiwa tattalin arzikinsu ba karami ba ne. Yace idan da mutum na kashe jaka guda a gidansa yanzu in ya kashe dala hamsin ya ci sa'a. Yana cewa masu sayar da ruwa, zogale, wake da dai ire irensu duk kasuwarsu ta mutu. Haka lamarin yake a duk Agadez.
Gwamnati ta yiwa masu sana'o'in alkawarin sama masu jari sai dai har yanzu shiru kamar an shuka dusa. Sun zurawa Allah idanu suna jira.
Jarkoki, igiyoyi, sanduna su ne aka fi anfani dasu a harkar bakin haure. Masu sayar dasu sun koka saboda rashin kasuwa lamarin da ya jefasu cikin wani mawuyacin hali. Masu sana'ar suka ce an dauki sunayensu da alkawarin kyautata masu lamura amma an yi watsi dasu.
Matasa ma suna korafin an dakatar da ayyukansu na samun abun biyan bukatunsu ta yau da kullum saboda haka suke rokokon gwamnati ta taimaka masu da abun yi.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Facebook Forum