Su dai ma’aikatan dake rike da kwalayen dake dauke da kalaman Allah-Wadai ,sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da kargame sakatariyar gwamnatin jihar inda suka zargi gwamnatin jihar da yin kunnen uwar shegu game hakkokinsu.
Wannan zanga-zangar dai na ma ko zuwa ne a kasa da mako guda da borin da yan kungiyar kwallon kafan jihar na maza da mata suka yi domin nuna fushinsu na rashin biyansu albashi na tsawon watanni.
Comrade Peter Gambo dake zama shugaban kungiyar kwadagon jihar yace,tura ce ta kaisu bango.
Da yake lallashin ma’aikatan shugaban ma’aikatan jihar Taraba Samuel Angyu, ya ce gwamnati na sane game da wannan matsalolin da ma’aikatan jihar ke fama da su na rashin albashi.
‘’ I, gwamnati na sane da matsalolin da ma’aikata ke fama dasu, nan bada jimawa ba,za’a magance wannan matsalar.Muna son ayi hakuri.Ai muna tattaunawa da shugabanin kwadago,suma sun san matsalolin ai.
Jim kadan da kamala wannan cincirindo,sai ga gwamnan jihar Taraban Darius Dickson Isiyaku ya bulla a majalisar dokokin jihar don mika kasafin kudin na shekarar 2017,inda ya bayyana cewa ba wani ma’aikaci dake bin gwamnatinsa bashin albashi koda kwandala ne.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.