Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Jihohin Kudancin Najeriya Sun Yi Taro a Lagos


People run as dust rises after explosions hit Aden airport, upon the arrival of the newly-formed Yemeni government in Aden.
People run as dust rises after explosions hit Aden airport, upon the arrival of the newly-formed Yemeni government in Aden.

Gwamnoni 17 daga jihohin kudancin Najeriya ne suka yi taro a karkashin jagorancin gwamnan jihar Lagos, wanda kuma a karshen taron, yace sun amince Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya “madaurinki daya” koda yake akwai bukatar da a sake fasalin kasar

Gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode shi ne ya jagoranci taron tare da gwamnan jihar Akwa Ibom.

Gwamnonin jihohin kudancin Najeriya su 17 suka samu halartar taron wanda shi ne na farko tun lokacin da tsohon gwamnan Lagos, Asiwaju Bola Tinubu ya jagoranci irin wannan taron na gwamnonin a shekarar 2005.

A sanarwar bayan taron da gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode ya karantawa manema labarai, ya bayyana matsayin da suka dauka na goyon bayan Najeriya ta kasance kasa daya. Sai dai kuma ya ce gwamnonin sun yi kira da a sake duba fasalin kasar.

Al’ummar yankin na kudancin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu akan taron inda suka bayyana ra’ayoyi iri-iri.

Gwamnonin sun kuduri yin taro na gaba a jihar Rivers.

Babangida Jibrin nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG