Gwamnonin da suka rufawa shugaba Buhari baya zuwa China na ganin tafiyar tayi tasiri kuma tana da alfanu garesu da kasar gaba daya.
Bayan ribar da gwamnatin tarayya zata samu suma gwamnoni suna da nasu rabon da suka samo a ziyarar.
Gwamnan jihar Adamawa Sanata Bindo Jibrilla dake cikin tawagar shugaban kasa da suka fara tafiya domin sharewa shugaban fage yace shugaban Najeriya ya damu da wahalar da talakawa ke sha saboda haka kasar zata karkata zuwa hanyar noma domin a samu wadatar abinci har ma a kai kasashen waje. China zata taimaka a wannan.
Yace nan ba dadewa ba za'a fara kawo kayan aikin noman zamani daga China yadda abinci zai wadatu a kasar.
Su ma 'yan majalisun dokokin jihohi sun nuna goyon bayansu game da ziyarar shugaban. Onarebul Hassan Marguma shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Adamawa yace yanzu gwamnatin tarayya ta amince a fara anfani da kudin China a kasar. Kasar zata bar anfani da dalar Amurka. 'Yan Najeriya na iya bude asusun yen da nera.
Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya yace irin matakan da shugaba Buhari ke dauka domin tada tattalin arzikin kasar sun dace. Yace tilas ne kuma kasar ta karbi bashi. Ko kasar Amurka tana ciwo bashi.
Ga karin bayani.