Gwamnatocin jihar Lagos da Ogun sun amince da hada hannu wajen gudanar da allurar rigakafin shan inna da kuma gamgamin wayar da kan al’ummomin jihohin a kan iyakokin kasar bi da bi, kan ciwon shan inna.
Gwamnatocin jihohin sun bayyana cewa, wannan zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta a cimma nasarar shawo kan cutar shan inna a kasar baki daya.
Kwamishinan lafiya na jihar Lagos Dr. Jide Idris ne ya bayyana haka a wata sanar inda yace shirin zai kunshi yiwa kananan yara allurar rigakafi a kan iyakokin dake tsakanin jihohin biyu.
Bisa ga cewarshi, gibin da ake samu a rigakafin shan inna yana faruwa ne a kan iyakokin jihohi inda ake kuskure tsallake kananan yara ba tare da an yi masu rigakafi ba.
Dr. Jide ya bayyana takaicin ganin yadda ake tsallake iyalai da dama lokacin rigakafin sabili da wadansu kananan hukumomi basu daukar wannan nawayar, ko kuma rashin maida hankali kan wadanda suke zaune a garuruwa da kauyukan dake kan iyakoki wajen aiwatar da shirin rigakafin.
Bisa ga cewarshi, hada hannu tsakanin jihohin dake makwabtaka da juna zai taimaka wajen shawo kan cutar shan inna a kasar da ta kasance daya daga cikin kasashe hudu a duniya da har yanzu ake kara samun yaduwar cutar.