A yayin da jihohi suka fara daukar matakan mayar da almajirai jihohinsu na asali, mazauna Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja sun fara nemar bayani a kan matakin da Minista Muhammad Bello zai dauka a kan almajirai da jihohi za su iya maida gida, Abuja.
Batun almajiranci, abu ne da ya jawo cece-kuce tsakanin al’umman jihohin arewa da dama, inda yawanci masana a fannin ilmin addinin islama ke yin tir da salon koyar da almajirai na zamanı da aka hada da barace-barace, sabanin yadda ya ke kafin lokacin mulkin mallaka.
A cikin tarihin arewacin Najeriya kafin lokacin mulkin mallaka, ba a san almajirai da yin barace-barace ba, lamarin da wasu daga cikin al’umman Najeriya ke dangantawa da rashin iya jagoranci, maida sarautar gargajiya karkashin ikon kananan hukukomi da dai sauransu.
A lokacin da cutar korona ke cigaba da yi wa jihohin Najeriya katutu, mazauna Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja sun fara kokawa a kan yadda aka bar almajirai a baya wajen kulawa.
Cikin masu kokawar har da wani fitaccen marubuci a fannin addini, Ghazali Muhammad Mijinyawa, wanda ya bayyana cewa nauyin kula da almajirai ya dogara ne a kan iyaye, shugabanni da asuran masu ruwa da tsaki.
Haka kuma, wani malami a makarantar boko da arabiyya na An-noor, Muhammad Sagir Assalafi, ya danganta kai yara almajiranci da iyaye ke yi da talauci inda ya bukaci gwamnati ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tallafa wa iyayen wadannan yara.
Shi ko wani almajiri dake karatun Arabiyya a yankin Mpape na Abuja mai suna Muhammad Muhammad ya ce bai san ko mene ne cutar covid-19 ba, kuma idan gwamnatin zata maida shi Kano wajen iyayensa, zai yi farin ciki matuka.
Duk kokarin ji ta bakin Ministan Birnin Tarayya, Abuja dai ya ci tura.
A cikin littattafan tarihi dai, Kalmar almajiri ya samo asali ne daga kalmar Larabci ta “Almuhajiru” dake nufin dan cirani mai neman ilmi, kuma daga masarautar Borno aka faro, inda a baya ba a bautar da yara almajirai.
A baya-bayan nan ne gwamnati ta mayar da almajirai sama da ashirin gida Kaduna inda akalla 21 suke dauke da kwayar cutar covid 19.
Ga Halima Abdulrauf da cikakken rahoton:
Facebook Forum