Wannan dai zai zama zakaran gwajin dafin sauya al’amura a kasar da shugaba Mohammdu Buhari ya yi lokacin yakin neman zabe.
Ko a sakon shugaban na bukin Easter, ya bukaci ‘yan kasar su kara hakuri yayinda yake yaki tukuru wajen ganin al’umma sun sha romon damokaradiya, da kuma hukumta masu almundahana.
A cikin jawabin nasa, shugaba Buhari yace “wannan gwamnatin tamu ba zata zama gwamnatin damokaradiya a baki kadai ba, amma har da ayyuka zahiri da ya hada da hulda kai tsaye da talakawa. Babu shakka a lokutan baya, kasar ta dandana kudarta a kan rashin adalci, ga kuma matsalar ‘yan ta’adda yayinda muke gwaggwarmayar daidaita lamutan damokaradiya.”
Wadanda wakilin Hausa ya yi hira da su , sun bayyana bukatar ganin shugaban kasar ya yiwa kowa adalci ba tare da nuna banbanci ba kasancewa ya sami kuri’u daga al’ummar Najeriya na kowanne bangare.
Gwamnatin dai zata fara aiwatar da ayyukan da tayi alkawari yayin yakin neman zabe ne bayan watanni goma da hawan karagar mulki.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Saleh Shehu Ashaka ya aiko daga Abuja, Najeriya.