Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bayyana Niyarta Ta Kauda Cutar Shan Inna Kafin Karshen 2013


Rigakafin cutar shan inna
Rigakafin cutar shan inna

Gwamnatin jihar Jigawa zata yiwa yara miliyan 1 allurar rigakafn cutar shan inna, a ci gaba da shirin allurar rigakafi.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake bayyana niyarta ta kawar da cutar shan inna a yankunan dake da hatsarin kamuwa da cutar ko kuma wuraren da aka sami bullar cutar kafin karshen shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Dr. Ado Mohammed, Directan hukumar lafiya matakin farko ne ya bayyana haka a ziyarar sa da ya kaiwa sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Sunusi.

Dr. Mohammed yace gwamnati tana kara karfafa allurar rigakafi da kuma fadakar da jama’a kan yadda ake daukar cutar da hanyar kare ta.

Ya kara da cewa, kananan hukumomi 12 ne cikin takwas suke da cutar sosai a cikin wata bakwai da suka wuce, kuma jihohi 28 basu da cutar ko kadan.

Ya kuma ce, “wannan ya nuna an sami raguwar kashi 70% idan aka kwatanta da shekara ta 2012.

Directan yace daukar wannan matakin ya biyo bayan alwakarin da gwamnonin jihohin da aka samu bullar cutar suka yin a daukar matakin shawo kanta. Ya kuma bayyana cewa, an dauki watanni bakwai ba a sami bullar cutar ba a jihar Jigawa.

Ya gargadi sarakunan gargajiya kada suyi kasa a gwiwa, akan sauran cututtukan dake kashe kananan yata kamar bakon dauro da sankarau.

A bayanin sa, sarkin Dutse yace bai yi mamaki ba a nasarar da aka samu a jihar saboda kokarin da gwamnatin tayi wajen yakin cutar shan inna.
Sarki ya kuma yi kira a cigaba da aiki da gwamnatin tarayya domin kawadda cututtukan.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG