Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya ta Mayarda Arewa Maso Gabashin Najeriya Saniyar Ware


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar kudancin Borno ya zargi gwamnatin tarayya nuna bangaranci ganin yadda ta mayarda yankinsa saniyar ware

Sanato Muhammed Ali Ndumi mai wakiltar kudancin Borno ya zargi gwamnatin shugaba Jonathan da mayarda jihohin arewa maso gabas saniyar ware a gudanar da mulkin Najeriya.

Sanato Ndumi ya ce abun damuwa ne matuka kan irin halin da mutanen yankin ke ciki. Ya ce duk da suna cikin mugun talauci amma babu wani abu takamaimai da gwamnati tarayya ta yiwa shiyar ganin cewa a bayyane take cewa shiyar ce tafi kowace talauci kuma yankin ne ke cigaba da fama da tashe tashen hankula da hare-haren 'yan bindiga. Ya ce an yi kone kone da kashe kashe. Manya manyan kasashen duniya sun ce ya kamata a bada taimako na musamman ga shiyar domin a habbaka arzikin yankin a kuma tallafawa mutane.

Yankin arewa maso gabas na cikin kidigdigar da hukumar majalisar dinkin duniya ta yi inda ta nuna cewa yankin na cikin wadanda talauci ya fi yi masu katutu a duniya. Sabili da haka ma Ndume ya ce yakamata gwamnatin tarayya ta dauki wani mataki musamman. Amma gwamnati na nuna masu wariya kamar yankin baya cikin Najeriya. Ya ce duk 'yan Najeriya suna karkashin shugaban kasa. Hakin kowa na kan shugaban kasa. Kowane bangaren Najeriya nada haki a kasar. Ya ce ba wai an mayarda su saniyar ware ba ma gwamnatin ta yi watsi da su. Ya ce a akasarin gaskiya ba'a yi masu adalci ba.

Taimakon nera biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta baiwa shiyar tamkar digo ne domin bai taka kara ya karya ba a ganin Sanato Ndumi.

Ga cikakken rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG