Dr. Umar Ardo yace kodashike ba wannan gwamnatin Jonathan ce ta janyo wa kasar tashe tashen hankula da ake fuskanta ahalin yanzu, amma ta kasa kare rayukan al'uma da dukuyoyinsu.
Dr. Ardo yace, ana kashe mutanen jihar ana korarsu daga gidajensu , wasu sun shiga dazuzzuka wasu kuma suna gudun hijira, saboda haka yake tambayar amfanin ko alfanun gwamnatin Jonathan ga jihar Adamawa da har wani zai tallata shugaban da nufin a sake zabensa. Dr. Ardo yace ta yaya za'ace mutum mai hankali zai goyi bayan gwamnatin da ta kasa kare jama'a, a sake zaben shugaban domin a ci gaba da tabbatar da jama'a suna cikin kunci?
Mafiya yawa daga cikin jama'a da Sashen Hausa ya zanta dasu, domin neman jin ra'ayoyinsu dangane da shirin sabunta 'dokar ta baci', sun bayyana rashin goyon bayansu da daukan wannan mataki.
Ga karin bayani.